Damarku ta cin nasara
Idan kun sayi tikiti ɗaya, damarku ta cin nasara 1 ce cikin miliyan 13.98. Don ku fahimci haka, ku ɗauka waɗannan bahon wanka uku sun cika da ƙwayoyin alkama kimanin miliyan 13.98, ƙwaya ɗaya ga kowane sakamako, kowace ƙwaya an rubuta mata lambobinta 6. Ku ce wa wani ya sa hannu, ya ɗauki ƙwaya ɗaya tak, ku yi fatan ita ce mai lambobinku. Don haka gara ku bar tikitin ku sayi tuffa.